Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Cristiano Ronaldo ya zama gwarzan dan wasa firimiyar Ingila na watan Satumba

Published

on

Dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo ya lashe gwarzan dan wasa na watan Satumba a gasar Firimiya ta kasar Ingila.

Ronaldo wanda ya dawo kasar Ingila a kakar wasannin da muke ciki bayan fafata wasa a kungiyoyin  kasashen Sifaniya da Italiya ya doke dan wasa Mohamed Salah, Allan da  Saint-Maximin, Antonio Rudiger, Joao Cancelo da kuma Ismaila Sarr

Ronaldo wanda ya koma  filin wasa na Old Trafford a watan Agustan da ya gabata, bayan da ya fara buga wasa a watan Satumba a wasan da Manchester United tayi nasara akan Newcastle da ci 4 da 1.

Haka zalika dan wasan ya taba zama gwarzan dan wasan wata a  kungiyar  a lokacin tsohon mai horar da tawagar Sir   Alex Ferguson.

Cristiano Ronaldo ya lashe gwarzan dan wasanne a karon farko tun a watan Maris din shekarar  2008.

‘Yan wasa  Sergio Aguero (7),  da Steven Gerrard ne suka lashe kyautar har sau  7 yayinda dan wasa Harry Kane ya lashe sau 6 sai kuma Cristiano Ronaldo ya lashe sau  (5)

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!