Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Cutar Coronavirus ta janyo faduwar danyan mai a Duniya

Published

on

Farashin gangar danyen mai na ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya sakamakon sabanin da ke tsakanin kasashen Saudiya da Rasha da kuma bullar cutar Corona.

An rika sayar da man fetur samfarin Bonny light na kasar nan, akan farashin dala talatin da bakwai da santi ashirin da biyu, maimakon dala arba’in da shida da aka rika sayarwa a shekaran jiya.

A baya-bayan nan ne dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki, don tattauna halin da kasafin kudin kasar nan na bana zai shiga, sakamakon faduwar farashin na danyen mai.

Haka zalika, ita ma majalisar wakilai, ta kafa kwamiti na musamman wanda zai nazarci illar da bullar cutar Corona ta yi ga tattalin arzikin ta bangaren janyo faduwar farashin gangan danyen mai.

Tun farko dai gwamnatin tarayya ta yi kasafin kudin bana ne akan dala hamsin da bakwai akan gangan danyen mai guda, sannan da tsammanin za a rika fitar da ganga miliyan biyu da dubu goma sha takwas a duk rana.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!