Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bayan rahoton Freedom Radio, Majalisar dokokin Kano ta yi sammacin shugaban hukumar tattara haraji

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano, ta yi sammacin shugaban hukumar tattara haraji na jihaar Abdurrazaƙ Datti Salihi.

A baya-bayan nan dai Freedom Radio ta yi wasu jerin rahotanni kan wata ƙididdiga da Mujallar Economic Confidential ta fitar da ya nuna Kano na samun koma baya a wajen samun kuɗin shiga.

Majalisar ta buƙaci shugaban da ya gurfana a gabanta domin yi mata bayani kan yadda hukumar ke tattara kuɗaɗe.

Kiran ya biyo bayan buƙatar da shugaban masu rinjaye Alhaji Labaran Abdul Madari ya gabatar.

Madari ya ce, kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa majalisar damar yin sammacin duk mai riƙe da muƙamin da ake nema kan ya bayyana gabanta domin share mata tantama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!