Connect with us

Labarai

Jarumin barkwanci Ahmad Aliyu Tage ya rasu

Published

on

Allah ya yiwa Ahmad Aliyu Tage rasuwa guda daga cikin jaruman masana’antar Kannywood.

Jarumin ya rasu a Litinin din nan, bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

Darakta a masana’antar Aminu S. Bono Dandago ne ya tabbatar da hakan a zantawar sa da Freedom Radio.

Kafin rasuwar sa Ahmad Tage yana cikin masu bada umarni a masana’antar da kuma daukar hoto baya ga yadda yake fitowa a fina-finan barkwanci.

Aminu S. Bono ya ce “Ahmad Tage yana da hazaka matuka domin kuwa duk irin rawar da aka bashi ya taka a cikin fim yana yin fiye da abinda ake bukata, kuma shi ne mutum na farko da ya sanya ‘ya’yan sa guda 5 a cikin harkar fim”.

“Tage yana da kwarewa kuma yana da barkwanci bashi da saurin fushi kuma bashi da son zuciya, don haka duniyar fim ba zata taba mantawa da shi ba” a cewar S. Bono.

Ana sa ran za a yi jana’izar sa da yammacin nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!