Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya umarci dukkanin ministocin da suke son takara su ajiye muƙamansu
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umurci ɗaukacin mambobin majalisar zartaswar tarayya da su ke neman takara a zaɓen 2023 su ajiye muƙaman su.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ya tabbatarwa Freedom Radio umarnin.
Ya ce, masu neman takarar da su gaggauta mika wasikunsu na yin murabus daga aiki kafin ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022.
“Misali kamar ƙaramin ministan ilimi Eka Nwajuaba da ya fara’a neman takara sai miƙa takardar ajiye aiki, kuma tunda shugaba Buhari yace su gaggauta ajiyewa ai kowa zai fuskanci gaggawar da ake nufi”.
Tun da fari dai ministan yaɗa labarai da raya al’adu Lai Mohamed ne ya fara sanar da hakan a ranar Laraba yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya.
Ya ce umarnin ya cire mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo saboda shi zaɓaɓɓen mamba ne a majalisar ministoci.
Ministan ya tabbatar da cewa idan akwai wasu gyare-gyare ko kari a cikin wannan umarnin za a yi su nan ba da jimawa ba.
A cewar Ministan, umarnin zai iya haɗawa da masu riƙe da muƙaman siyasa, idan buƙatar hakan ta taso.
You must be logged in to post a comment Login