Labarai
Da ɗumi-ɗumi- Kotu ta yankewa Faruk Lawan hukuncin shekaru 7 a gidan yari
Wata babbar kotun birinin tarayya Abuja da ke da zama a unguwar Apo, ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari ga tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Ɓagwai da shanono, Faruk Lawan.
Hukuncin ya biyo bayan kama shi da laifin karɓar na goro a hannun fitaccen ɗan kasuwar nan Femi Otedola.
Mai shari’a Angella Otaluka yayin yanke hukuncin, ta ce ta gamsu da hujjojin da hukumar yaƙi da cin hanci da rasha ta ICPC ta gabatar a gaban kotu da ke cewa, tsohon ɗan majalisar ya karɓi na goron dala dubu ɗari biyar a wajen ɗan kasuwar.
A cewar ta, ta ɗaure Faruk Lawan shekaru bakwai a laifuka na farko da na biyu, yayin da ta yanke mishi hukuncin ɗaurin shekaru biyar a laifi na uku. Sai dai hukunce-hukuncen guda biyu za su riƙa tafiya ne a tare.
You must be logged in to post a comment Login