Labarai
Da an binciko masu hannu a kisan Ruƙayya Ɗanbare za su fuskanci hukunci – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta tabbatar an binciko tare da hukunta waɗanda ake zargi da kashe wata matar aure mai suna Rukayya Mustapha har gidanta da ke unguwar Ɗanbare anan Kano.
Gwamnan Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a ranar Litinin lokacin da tawagar gwamnatin Kano ta kai ziyarar ta’aziyyar gidansu marigayiyar.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Nasir Yusuf Gawuna ya tabbatar da cewa, gwamnati ba za ta saurarawa duk wasu masu aikata ta’addanci ga al’ummar da basu ji-ba basu-gani ba.
“Ba za mu zuba idanu rayukan al’umma ya zama tamkar na kiyashi ba, a don haka duk wanda aka samu da laifin kisan kai gwamnati za ta gaggauta ɗaukan mataki a kansa” a cewar Ganduje.
Da asubahin ranar Lahadi wasu da ba a san ko su wanene ba suka shiga gidan matar auren tare da yi mata duka da makamai har sai da rai yayi halinsa.
You must be logged in to post a comment Login