Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Da dumi-dumi: EFCC ta cafke Muntari Ishaq Yakasai

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa shiyyar Kano EFCC ta cafke kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Kano Muntari Ishaq Yakasai bisa zargin karkatar da naira miliyan saba’in da shida mallakar karamar hukumar birni a lokacin da yake shugabantar karamar hukumar.

Kamun da aka yi masa ya biyo bayan takardar korafi da wasu suka rubuta akan sa kan zargin karkatar da kudaden da aka ware domin wasu ayyuka a karamar hukumar.

Har ila yau ana zarginsa da gine wani sashe na makarantar Firamare ta Kofar Nassarawa inda ya gina shaguna ya siyar dasu akan kudi Naira miliyan goma-goma sannan ya turmutsa kudin.

Sanarwar mai dauke da sa hannu Tony Orilade mai rikon mukamin jami’in yada labarai na hukumar ta EFCC shiyyar Kano ta bayyana cewa zasu gurfanar dashi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!