Connect with us

Labarai

Da dumi-dumi: Mutane 14 ciki har da kananan yara sun kone kurmus a hatsarin mota

Published

on

Mutane goma sha hudu (14) ciki har da kananan yara 3 sun kone kurmus sakamakon hatsarin mota da ya faru a titin Ibadan zuwa Lagos

 

Rahotanni sun ce hatsarin ya ritsa ne da wata mota kirar Toyota RAV 4 mai lamba LND 13 GS da kuma wata motar itama kirar Toyota Camry mai lamba GGE 369 GJ da kuma wata motar safa kirar Mazda.

 

Kuma hatsarin ya faru ne da misalin karfe goma da mintuna ashirin na daren jiya

 

Mai magana da yawun hukumar kiyaye abkuwar hadurra ta jihar Lagos Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!