Connect with us

Labarai

Dakarun Operation Hadin Kai sun dakile harin ISWAP a Yobe

Published

on

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta JTF da ke aiki a Arewa maso Gabashin Najeriya karkashin rundunar Operation Hadin Kai, sun samu nasarar dakile hare-haren da ake zargin mayakan ISWAP ne suka kai a Jihar Yobe.

 

Haka kuma, Dakarun sun kashe sama da mahara 20 ciki har da babban kwamandan kungiyar mai suna Abu Yusu.

 

Yan bindigar sun yi niyyar kai farmakin ne kan sansanin dakarun da ke Goniri, karkashin shiyya ta 2 ta rundunar sojin a daren ranar Litinin 9 zuwa safiyar Talata 10 ga watan nan da muke ciki na Maris.

 

Sojojin sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwar, Sani Uba, ya fitar.

 

Sanarwar ta ce ‘yan ta’addan sun yi kokarin kai farmaki ta hanyoyi da dama a lokaci guda domin kewaye sansanin dakarun sai dai ba su samu nasara ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!