Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP 50

Published

on

Rundunar sojin ƙasar nan ta ce dakarun ta sun samu nasarar kashe aƙalla kwamandoji da mambobin ƙungiyar ISWAP 50 a wani farmaki da suka kai a ƙaramar hukumar Askira Uba a jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar birgediya janar Onyema Nwachukwu ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Nwachukwu ya ce, dakarun sojin haɗin gwiwa da na Operation Haɗin kai da ke Arewa maso Gabas sun yi nasarar kashe ‘yan ta’addar kungiyar ISWAP sama da 50 tare da lalata kayan da suke ta’addanci da su .

Sojojin sun kuma yi luguden wuta kan motar ‘yan ta’addan da kuma wata motar sulke.

Idan dai za a iya tunawa a ranar Asabar din da ta gabata ne yan ta’addar na ISWAP suka kai hari a wani sansanin soji da ke Askira Uba, tare da yin kwanton ɓauna inda suka kashe birgediya janar Dzarma Zirkushu da wasu sojoji uku.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!