Labarai
Dakarun Operation Hadin Kai sun tarwatsa sansanin yan ta’adda a Sambisa

Dakarun Rundunar Sojin Najeriya na Operation Hadin Kai, sun kai wani hari ta sama inda suka tarwatsa wani sansanin ’yan ta’adda ne a dajin Sambisa a jihar Borno.
Wannan na cikin wata sanarwar da Daraktan hulɗa da jama’a na Rundunar Sojin Sama Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa, aikin ya biyo bayan leƙen asiri da aka gudanar a yankin Kashomri da Sambisa, inda bayanan suka nuna motsin ’yan ta’adda a wasu gine-gine da suke amfani da su a matsayin maboya.
Ya ce, jiragen rundunar sun kai hare-hare ta sama kan wuraren da aka tabbatar suna da alaƙa da ayyukan ’yan ta’adda, bayan tattara sahihan bayanai daga jiragen leƙen asiri da bayanan sirri.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, dakarun za su ci gaba da ayyukan da suka shafi tabbatar da tsaro a yankunan da abun ya shafa.
You must be logged in to post a comment Login