Labarai
Dakarun Soji na rundunar Operation MESA sun hallaka ƴan bindiga 19 a Kano

Dakarun rundunar sojin Najeriya, sun samu nasarar murkushe wasu ƴan bindiga da kuma wani yunƙurin da suka yi na kai hari a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Shanono a jihar Kano.
Rundunar sojin sama ta Operation MESA, da ke ƙarƙashin birged na uku da ke Kano ne suka jagoranci aikin bayan samun bayanan sirri da suka ce sun samu kan yunƙurin ƴan bindigar na kai harin.
Wata sanarwa da jami’in yada labaran sashen, Babatunde Zubairu ya fitar, ta ruwaito cewa, ƴan bindigar sun shiga a ƙauyen Unguwan Tudu da Unguwar Tsamiya da Goron Dutse a ƙaramar hukumar Shanono da misalin ƙarfe biyar na yamma a ranar 1 ga watan Nuwamba.”
Sanarwar ta kara da cewa, an samu nasarar kashe ƴan bindiga 19 a gumurzun, sai dai sojoji guda biyu, sun rasa rayukansu.
Kwamandan sashen Birgediya Janar Ahmed Tukur ya buƙaci mutanen yankin su ci gaba da gudanar da harkokinsu, sannan ya yi kira gare su da su riƙa sa ido kan abubuwan da ke wakana tare da kai musu bayani da gaggawa.
You must be logged in to post a comment Login