Labarai
Sojoji sun dakile hari da ’yan ta’addan ISWAP suka kai a Jihar Borno

Rundunar sojin kasar nan, ta ce dakarunta sun daƙile wani hari da yan tada kayar baya na ISWAP suka kai kan sansanin soji da ke Auno a jihar Borno, tare da kaddamar da harin ramuwar gayya wanda ya lalata kayan yaƙin da ‘yan ta’addan ke yin amfani da su.
Rundunar ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar wa manema labarai.
Sanarwar ta bayyana cewa, a daren ranar 5 ga watan nan da muke ciki na Fabrairu ne yan ta’addan ISWAP suka kai hari kan wani sansanin sojoji amma Sojojin sun dakile harin cikin tsari da ƙwarewa.”
Bayan daƙile harin, a ranar 9 ga Fabrairu, sojojin tare da hadin gwiwar dakarun sa kai ta CJTF suka ƙaddamar da samame ta ramuwar gayya a kan mayaƙan ISWAP ɗin a layin Komala da ke ƙaramar hukumar Konduga.
You must be logged in to post a comment Login