Labarai
Dalibai 30 ne suka koyi sana’o’in dogaro da kai a Wudil
A yau Lahadi ne makarantar al’umma ta Bahaz Integrated Academy dake garin Wudil a nan Kano ta yaye dalibai guda talatin 30 da sukaci gajiyar koyon sana’o’in dogaro da kai.
Daliban da aka yaye sun samu koyon sana’ar dinki da makarantar ta shirya, Inda aka raba musu takardun shaidar koyo da kuma kyaututtuka.
Da yake jawabinsa a yayin taron shugaban makarantar Malam Bilyaminu Usman Usman ya bayyana cewa ba komai ne ya sanya su yin wannan aiki ba sai kokarin samarwa da al’umma ayyukan yi, domin magance zaman banza.
Malam Bilyaminu ya kara da cewa daga cikin abubuwan da suke koyarwa ga daliban makarantar sun hadar da hada Takalmi, Jaka, Kiwon Kifi da Kiwon Kaji da kuma koyar da amfani da na’ura mai kwakwalwa wato Kwamfiyuta.
Su ma wasu daga cikin daliban da suka amfana da koyarwar sun shaidawa Freedom Radio farin cikin su, tare da godiyarsu ga hukumar makarantar.
Daga cikin mahalarta taron sun hada da wakilin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, wanda kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya wakilta, da shugaban karamar hukumar ta Wudil Mallam Saleh Kausani da sauran iyayen yara da al’ummar garin ta Wudil.