Labarai
Dalibai masu lalurar gani 337 ne a yau su ke rubuta jarabawar JAMB a Nijeriya
- Farfesa Muhammad Yahuza Bello ne ya bayyana hakan a yau, lokacin da yake Jawabi yayin shirye-shiryen fara jarabawar
- ya ce, ‘a cikin cibiyoyi 11 da ake da su a kasar nan, jihar Kano ce ke kan gaba da dalibai 88 wadanda za su rubuta jarabawar
- Cikin abubuwan da aka tanadar wa daliban akwai takadda mai rubutu da allura, da na’urar rubutu ta tafiraita
- Daliban da suka zauna domin zana jarabawar, sun bayyana cewa ‘sun yiwa jarabawar shiri na musamman
Kimanin dalibai masu lalurar gani 337 ne za su rubuta jarabawar shiga manyan makarantun kasar nan JAMB a kasar.
Mai kula da jarabawar a jihar Kano, kuma malami a jami’ar Bayero Farfesa Muhammad Yahuza Bello ne ya bayyana hakan a yau, lokacin da yake Jawabi yayin shirye-shiryen fara jarabawar a cibiyar da aka warewa masu lalurar gani da ke Goron Dutse.
Farfesa Yahuza Bello ya ce, ‘a cikin cibiyoyi 11 da ake da su a kasar nan, jihar Kano ce ke kan gaba da dalibai 88 wadanda za su rubuta jarabawar a bana’.
Wanda ya ce ‘duk wani shirye-shiryen da ya kamata ayiwa daliban da zai saukaka musu rubuta jarabawar anyi shi’.
‘Cikin abubuwan da aka tanadar wa daliban akwai takadda mai rubutu da allura, da na’urar rubutu ta tafiraita, da wani allon da zasuyi amfani dashi yayin zana jrabawar’.
‘Haka zalika an tanadi wadanda zasu rinka karantawa daliban takardar dake dauke da tambayoyin idan bukatar hakan ta taso’.
Farfesan ya ce ‘a yayin da aka shiga karo na bakwai da warewa masu bukata ta musamman cibiyar zana jarabawar shiga jami’ar ta JAMB, ana samun nasarori daban-daban na cigaba’.
Wanda ya ce ‘ya zuwa yanzu kason da ake samu na wadanda suke faduwa jarabawar JAMB din na masu gani, ya ninka na masu lalurar gani da ido’.
‘Hakan na nuni da cewa daliban masu lalurar ganin na da fakiri da fasaha ta musamman, don haka suna bukatar gudunmawar makusantarsu, don su cimma burikansu na rayuwa kamar kowanne dalibi’.
Daliban da suka zauna domin zana jarabawar, wadanda suka zo daga jihohi daban-daban a Arewacin kasar nan da suka hadar da Katsina, Zamafara sun bayyana cewa ‘sun yiwa jarabawar shiri na musamman, da suke sa ran samu nasarar da zata basu damar shiga jami’a’.
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login