Connect with us

Labarai

JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME na bana

Published

on

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta kasa JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME da dalibai suka rubuta a watan jiya na Afrilu.

Shugaban hukumar ta JAMB farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai yau Asabar a Abuja.

Farfesa Ishaq Oloyede ya kuma nemi afuwan al’ummar kasar nan sakamakon tsaikon da aka samu wajen fitar da sakamakon jarabwar.

Ya ce, an saki sakamakon dalibai miliyan daya da dubu dari bakwai da casa’in da biyu da dari bakwai da goma sha tara, yayin da kuma aka rike sakamakon wasu dalibai dubu talatin da hudu da dari daya da ashirin ciki kuwa har da wasu dubu goma sha biyar da dari daya da arba’in da biyar wadanda aka gano cewa tagwaye ne.

Ya kuma bukaci dalibai da su yi amfani da lambobin wayoyin su da suka yi rajista wajen aikawa da sako ta kan wannan lamba 55019, domin duba sakamakon su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,745 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!