Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

DSS ta kama shugaban tsaron gwamnan Adamawa

Published

on

  • Hukuma tsaro ta Nijeriya DSS ta kama Ahmad Umar shugaban tsaron gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, da mutane uku
  • Ana zargin hakan ya biyo bayan ganin bidiyon ‘yan siyasa na Jihar na zagin shugaban DSS din
  • Haka zalika da kuma bayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben kujerar gwamnan Jihar Adamawa

Hukuma tsaro ta DSS ta kama Ahmad Umar shugaban tsaron gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, da mutane uku magoya bayan jam’iyyar PDP, sakamakon zargin cin zarafin jam’inta da kuma jami’an hukumar zabe.

Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar ta DSS ta kama su ne a daren jiya alhamis.

Idan ba’a manta ba dai a baya cikin wani fefen bidiyo an ga wasu fusatattun ‘yan siyasa sun shiga Otal din Green City dake birin Yola, tare da cin zarafin babban jami’in DSS.

Hakan ya biyo bayan bayana sakamakon ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zabe, da dakataccen kwamishinan zaben jihar Hudu Yunusa-Ari ya yi a baya.

Rahoton: Ahmad Kabo Idris

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!