Labarai
Daliban da suka kammala karatu basu da kwarewa- Pro. Mustapha Bichi
Wani malami a jamiar Bayero da ke nan Kano, farfesa Mustapha Bichi, yace, kaso tamanin na dalibai da ke kammala karatu a jami’oi da sauran makamantun”gaba da sakandire a kasar nan ba sa samun alKin yi ne sakamakon cewa ba su da kwarewa da masu ba da aiki ke bukata.
Farfesa Mustapha Bichi wanda kuma malami ne a tsangayar nazarin Injiniya a jamiar ta Bayero, ya bayyana hakan ne ta cikin wata mukala da ya gabatar a makon sana’oi da cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da samar da ci gaba ta CITAD ta shirya a nan Kano.
Ya ce, akwai bukatar daliban kasar nan su rika neman ilimin sana’oi da kwarancewa a wasu bangarori da dama domin taimaka musu wajen samun gogewa da masu daukar aiki ke bukata.
Daliban jami’ar KUST zasu fara zuwa Amurka don karo ilimi
Ilimin sana’o’i shi ne mafita ga al’umma
Kano zata hada kafada da kasashen duniya a bangaren ilimi –Ganduje
Farfesa Mustapha Bichi ya kuma ce ya kamata dalibai su kwana da sanin wajibi ne kowa ya daura damara domin fuskantar kalubale da ke fuskantar wannan lokacin na a zauna a zura ido ana tsammanin kudin man fetur ya wuce saboda haka wannan al’umma su tashi tsaye don neman na kan su.