Connect with us

Labarai

Jami’ar Yusuf Maitama Sule zata yi bikin yaye dalibai

Published

on

Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke nan Kano, ta ce za ta yi bikin yaye dalibai dubu biyu da dari biyar da goma sha hudu a jibi Asabar din karshen makon nan.

Bikin yaye daliban dai ya hada da dalibai da suka kammala karatu a jamiar daga shekarar 2016 da 2017 da kuma 2018.

Shugaban jami’ar ta Yusuf Maitama Sule Farfesa Mustapha Ahmad Isa ne ya bayyana hakan yayin zantawa da jaridar Solacebase anan Kano.

Farfesa Mustapha Ahmad Isa ya kara da cewa, daliban da suka kammala jami’ar a bana ba za su shiga cikin bikin ba, kasancewar sun kammala jami’ar ne bada dadewa ba, ga kuma rashin fitowar sakamakon jarrabawa
karshe akan lokaci su na

Mustapha Ahmad Isa wanda Farfesa ne a bangaren turanci da kimiyyar harshe, ya ce jamiar ba za ta bada digirin girmamawa ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!