Labarai
Dalibar Jangebe da taga mahaifinta a hannun ‘yan bindiga ta samu nasarar ceto shi.
Mahaifin daya daga cikin daliban makarantar sakandire ta Jangebe da ke jihar Zamfara wanda ‘yarsa ta ganshi a hannun ‘yan bindiga a kwanakin baya ya shaki iskar ‘yanci.
Malam Iliya Gwaram wanda aka kawo shi gidan gwamnatin jihar Zamfara da ke Gusau da misalin karfe tara na dare a jiya litinin ya shaidawa manema labarai cewa shi da kanshi ya gayawa ‘yar tashi cewa karta nuna alamun ta gane shi bayan da ta ganshi a daure a sansanin ‘yan bindiga.
An dai samu nasarar ceto Iliya Gwaram ne shi da wasu mutane tara ciki har da wata mata mai shayarwa da kuma kananan yara uku.
Ya ce an kamashi ne da mutanen da aka ceto su tare tsawon watanni uku da suka gabata, inda sai kuma a wata ranar juma’a ce kawai bayan an kawo wasu daliban makaranta da aka sato su sansanin sai kawai yana juyawa sai yaga ‘yar sa cikin firgici tana kallonsa.
‘‘Daga nan sai kawai na gayawa wasu daga cikin daliban ‘yan makarantar da aka kawosu tare da ‘yata’ cewa su gayamata kar ta yadda ta nuna alamun ta sanni’’
Nayi hakan ne kuwa don gudun abin da ka iya faruwa da ita idan har suka san cewa ita ‘ya’ ta ce’’
‘‘Ban taba kuka ba a rayuwata kamar ranar da naga an zo za a tafi dasu saboda tunani na shikenan bazan sake ganin ‘ya’ taba har abada’’
‘‘’A rashin sanina ban san cewa ‘yar tawa ta zanta da gwamna Matawalle game da halin da ta ganni a ciki ba’’ acewar Malam Iliya.
You must be logged in to post a comment Login