Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Rundunar Sojin kasar nan ta gargadi Sheikh Gumi da ya rika kyautata kalamansa

Published

on

Rundunar sojin kasar nan ta ce babu kanshin gaskiya cikin zargin da ke cewa tana turawa da jami’anta zuwa aikin tabbata da tsaro ne bisa tsarin addini ko kabila

Mai magana da yawun rundunar Burgediya Janar Muhammed Yerima ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya litinin.

Muhammed Yarima ta cikin sanarwar dai ya ce, rundunar ta fitar da sakon ne don mai da martani kan kalaman da Shehin malamin ya yi abaya-bayan nan.

‘‘Saboda haka rundunar soji tana gargadin Sheikh Gumi da ya guji furta irin wannan kalamai da ke bata mata suna’’.

‘‘Duk wani aiki da rundunar sojin kasar nan za ta yi tana yinshi ne bisa kwarewa da sanin ya kamata saboda haka wani mutum yazo ya ce wai rundunar tana amfani da addini ko kabila wajen aiwatar da ayyukanta batu ne kawai marar tushe da bashi da makama’’ a cewar Yarima.

Rahotanni sun ce Sheikh Gumi dai ya yi zargin cewa rundunar sojin kasar nan tana turawa da sojoji wadanda ba musulmi ba don yaki da ‘yan bindiga da ke aikata ta’asa a yankin jihohin arewa maso yamma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!