Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kamata yayi a tsawaita dokar hana zirga-zirgar jirage zuwa wasu jihohin – ACF

Published

on

Kungiyar dattawan Arewa ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsawaita dokar hana zirga-zirgar jirgin sama a Zamfara da aka yi a baya-bayan nan zuwa wasu jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.

A jiya Talata ne Buhari ya ayyana Zamfara a matsayin “yankin da aka haramtawa jirage yin shawagi” sannan ya haramta duk wasu ayyukan hakar ma’adanai a jihar.

Umarnin, wanda mai ba shi shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno ya bayyana, ya biyo bayan sakin daliban 279 na Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Jangebe a karamar Hukumar Talata-Mafara da ’yan bindiga suka sace.

A wata sanarwa a yau laraba da shugaban kungiyar ta ACF Audu Ogbeh ya fitar na yabawa da umarnin, sai dai yace akwai bukatar yin irin wannan umarnin a wasu jihohi kamar Benue Taraba da Borno inda ake rade-radin cewa jirage masu saukar ungulu suna yawan ajiye makamai don ‘yan fashi da masu tayar da kayar baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!