Labarai
Dalilan da suka sanya Ganduje ya hana bara a Kano – Dr. Sa’idu Dukawa
Majalisar malamai ta jihar Kano ta alakanta yawaitar kananan yara da mata akan titina da cewa yana daya daga cikin abubuwan da ke haifar barace-barace, wanda hakan ya sanya gwamnatin jihar kano ta dauki gabarar hana bara a fadin jihar Kano.
Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa wanda guda ne daga cikin mambobin majalisar ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan tashar freedom rediyo.
Ya ce ba wai anan kasar ne kawai ake da mabarata ba hatta sauran kasahen duniya suma suna fuskantar matsalar, inda ya ce kamata yayi mutane su banbance yaran da ke karatu a tsangaya da kuma yaran da suke yawo da sunan bara a kan titunan jihar Kano.
Ya kara da cewa babu wani dalilin da zai sa a rika koyawa daliban makarantun tsangaya yaren turanci da kuma lissafi ba, domin an kafa makarantun tsangaya ne domin haddace al kur’ani da kuma rubuce shi.
Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa ya ja hankalin iyaye da cewa su rika sauke nauyin da All….. ya dora musu na kula yaran su da kuma tarbiyyantar da su.
You must be logged in to post a comment Login