Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Dalilan da suka sanya gwamnatin Kano za ta rufe wani Asibiti

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tayi barazanar garkame wani asibiti mai zaman kasan da ake Sahara da ke karamar hukumar Tarauni a nan Kano sakamakon rashin tsafta.

Hukumar kula da asibitoci masu zaman kan su ta jihar Kano tayi barazanar ne lokacin da take ran-gadin duba wasu asibitoci a jihar Kano.

Hakan na cikin wata sanarwar da babban sakataren hukumar Dakta Usman Tijjani Aliyu ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta bayyana cewa, sakamakon rashin tsaftar kayan kula da marasa lafiya a asibitin musamman a bangaren maza, inda hukumar ta lura da rashin tsafta a jikin katifun na marasa lafiya ke kwanciya da zannuwan gado da wasu sassa na asibitin.

Sanarwar ta bai wa hukumar asibitin wa’adin makwanni biyu da su tabbatar sun gyara matsalolin da hukumar ta zayyana na rashin tsafta a asibitin na Sahara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!