Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Ministan lafiya ya ce cutar corona ta yadu a kananan hukumomi 586

Published

on

Ministan lafiya Dr Osagie Ehanire ya ce cutar corona ta yadu a kananan hukumomi 586 cikin kananan hukumumomi 774 da ke fadin kasar nan.

Dr Osagie Ehanire na bayyana hakan ne a jiya, jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartaswa ta kasa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ministan ya bayyana damuwarsa kan yadda kawo yanzu cutar corona ke ci gaba da yaduwa tare da tabarbare harkokin tattalin arzikin kasar.

Ehanire ya kuma bayyana cewa, majalisar zartaswa ta amince da a kashe sama da naira biliyan takwas don sayan wasu kayayyaki guda 12 a hukumar NCDC don yaki da cutar, wadanda za a raba a cibiyoyin da ke gwajin cutar don bunkasa ayyukan su.

Ta cikin jawabin nasa, Ehanire, ya ce a yanzu haka wadanda suka kamu da cutar a kasar nan  sun kai dubu 47, 290 yayin da mutuane dubu 33, 609 suka warke, sai kuma wadanda suka rasu su 956 cikin jihohi 36 kamar yadda NCDC ta tattara alkaluman.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!