ilimi
Dalilan da suka sanya muka janye malamai – Ƙiru
Gwamnatin jihar Kano ta ce rashin malamai a makarantun gwamnati shi ne dalilin da yasa ta janye malaman da ta tura makarantun sa kai da kuma makarantun al’umma wato community schools.
Kwamishinan ilimi na jihar Malam Muhammad Sanusi Sa’idu Ƙiru ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.
Malam Muhammad Sa’idu Ƙiru ya kuma ce sakamakon janye malaman da gwamnatin jihar kano ta yi da yawa daga cikin makarantun al’umma sun dawo ƙarƙashin gwamnati.
“Dama can doka ba ta bada damar gwamnati ta kai malamai makarantun sa kai ko na al’umma, shi ya sa daga baya muka ga dacewar dawo da su makarantun gwamnati don su ci gaba da bada gudunmawaa” in ji Ƙiru.
Kwamishinan ya kuma jajjada cewa har yanzu tsarin bada ilimi kyauta kuma dole yananan a jihar Kano domin samar da ilimi ga kowa da kowa.
You must be logged in to post a comment Login