Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Gwamnatin Kano ta bada umarnin komawar sauran dalibai makaranta

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta amince da komawar dalibai ‘yan aji daya da na aji hudu na Sakandare makaranta a ranar Litinin mai zuwa.

Kwamishinan Ilimi na jihar Kano Malam Muhammad Sanusi Sa’idu ne ya bayyana hakan, yana mai cewa komawa makarantar ta shafi ‘yan makarantun jeka-ka-dawo da na kwana a makarantun gwamnati dana masu zaman kansu.

 

Sanusi Sa’idu Kiru ya ce daliban makarantun kwana za su koma makarantar ne a ranar 15 ga watan Nuwamba, inda kuma na makarantun jeka-ka-dawo za su koma a ranar 16 ga watan.

 

Sai dai ya bukaci, shugabannin makarantun da su gudanar da duk wasu shirye-shirye don komawar daliban makaranta.

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!