Labaran Kano
Dalilan da suka sanya shugaban kasa ke gabatar da kasafi
Wani malami a sashen koyar da harkokin tattalin arziki na kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi dake nan Kano Malam Abdussalam Kani, ya bayyana cewa gabanin gwamnati ta gabatar da daftarin kasafin kudi akwai abubuwan da take la’akari da su domin kauce wa samun matsala.
Malam Abdussalam Kani, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin’’Duniyar mu a Yau na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan kasafin kudin badi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisun Najeriya
Ya ce an kirkiro da tsarin na gabatar da kasafi domin kayyade adadin kudaden da gwamnati za ta kashe a shekara guda, kuma ana gina shi ne bisa hasashen kudin da ake tsammanin za’a samu.
Shi kuwa wani masanin hada-hadar kudade Malam Jamilu Abdussalam da ya kasance a cikin shirin, ya bayyana cewa, akwai alaka mai karfi tsakanin harkokin kasuwanci da kuma kasafin da gwamnati ke warewa, musamman ta fannin ababen more rayuwar al’ummar kasa.
Da yake tsokaci ta cikin shirin, wani kwararren Akanta Malam Ado Muhammad, wanda shi ne tsohon shugaban kungiyar kwararru ta kasa ICAN shiyyar Kano, ya ce duk lokacin da aka gabatar da kasafi akwai nazari da ake gabatarwa kan na shekerar da ake ciki da wacce ta gabata da kuma wadda ake sa ran za’a shiga da wanda akasari ake mika wa majalisun.
Akanta Malam Ado Muhammad, ya kara da cewa, ta hanyar yin nazarin kasafin ne ake iya gano yadda aka samu nasara ko kuma akasinta a tsawon shekaru uku da ake gudanar da nazarin.