Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalilan da ya sanya Ganduje ya soke bukukuwan sallah babba a Kano

Published

on

A kokarinta na tabbatar da samun nasarar yakar cutar Corona majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da soke dukkan bukukuwan Sallah da aka saba yi na Babbar Sallah

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Mallam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a yau lokacin da yake zantawa da manema labarai a wani bangare na bayyana abubuwan da aka tattauna a taron majalisar zartarwa na jiya.

Ya Kara da cewa dukkanin sarakunan masarutu biyar zasuyi sallar idi a masarautunsu ba tare da ziyarar gidan shettima ba da hawan Nassarawa da Daushe da sauran bukukuwan al’ada

Mallam Muhammad Garba ya Kara da cewa majalisar zartarwar a jiya ta kuma amince da Mika kuduri ga majalisar dokokin jihar nan don yin gyara akan dokar masarutu da sake yin duba ga kunshin karba karba na shugabancin majalisar sarakunan.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa kwamishinan ya kuma ce majalisar ta kuma amince da sakin fiye da naira miliyan 37 don aiwatar da Shirin koyawa Mata matasa guda 586 sanaoin gida na hannu daban daban.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!