Labarai
Dalilan da ya sanya Kotun Abu Dhabi ta yanke ma wasu ‘yan Najeriya daurin rai da rai
Babbar Kotun birnin Abu Dhabi na hadaddiyar Daular Larabawa ta zartarwa wasu ‘yan Najeriya guda hukuncin dauri a gidan Yari sakamakon samunsu da laifin taimakawa kungiyar Boko Haram da kudade.
Biyu daga cikinsu masu suna Surajo Abubakar Muhammad da Saleh Yusuf Adamu an zartar musu da hukuncin daurin rai-da-rai, yayin da sauran mutane hudun aka aka zartar musu da hukuncin daurin shekaru goma-goma a gidan Yari.
Mutane hudun sun hadar da Ibrahim Ali Alhassan da Abdulrahman Ado Musa, sai Bashie Ali Yusuf da kuma Muhammad Ibrahim Isa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an fara shari’ar mutunen tun a shakarar da ta gabata kafin zartar da wannan hukunci.
Kotun ta gano cewa mutanen sun tallafawa kungiyar Boko Haram da makudan kudade ta hanyar aikawa ta asusun banki.
You must be logged in to post a comment Login