Connect with us

Labarai

Dalilan da ya sanya Tambuwal zai maida kwalejin ilimi zuwa jami’a a Sokoto

Published

on

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya ce gwamnatin jihar zata daga darajar kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari zuwa matakin Jami’a.

Gwamna Tambuwal, ya bayyana hakane a jiya a lokacin gudanar da bikin cikar makarantar shekaru Hamsin da kafuwa.

Gwamnan ya bada umarnin gina sababbin dakunan kwana na Dalibai da zai dauki mutane sama da 400, wanda yace yin hakan ya biyo bayan tarihin da makarantar take dashi na samar da kwararru kuma fitattun malamai a fadin kasar nan.

Da yake nasa jawabin a wajen taron shugaban Kwalejin Dakta Wadata Hakimi,ya ce kawo yanzu haka makarantar ta yaye Dalibai sama da 48, 936 da suka samu shaidar kammala karatun NCE tun bayan kafa makarantar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!