Labaran Wasanni
Dalilin da ya sa aka cire Manchester United daga gasar FA Cup
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fice daga gasar kofin kalu bale na FA Cup, bayan rashin nasara a hannun Middlesbrough daci 8-7 a bugun daga kai sai mai tsaran gida.
Fafatawar dai an kwashe tsahon minti 120, bayan tin da fari an tashi wasa 1-1 karawar da ta gudana a filin Old Trafford a ranar Juma’a 04 ga Fabrairun 2022.
Dan wasa Anthony Elanga daga Middlesbrough ne ya zura kwallon da ta bawa tawagarsa damar kaiwa zagaye na gaba a gasar.
Tin a minti na 24 dan wasan Manchester United Jadon Sancho ya zura kwallon farko a ragar Middlesbrough’s
Kafin dan wasa M Crooks ya warware kwallon da aka zura musu a minti na 64 jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Sai dai ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United sun zargi alkalin wasa
Anthony Taylor da bayar da kwallon da aka zura musu ta hanyar duba na’urar VAR mai tai makawa alkalin wasa.
Zuwa yanzu dai za a raba jadawalin zagaye na biyar na gasar FA Cup a ranar Lahadi mai zuwa.
You must be logged in to post a comment Login