Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dan Najeriya ya shaki iskar ‘yanci a kasar Saudiya

Published

on

Wani dan asalin Jihar Zamfara mai suna Ibrahim Ibrahim da ke fuskantar hukuncin kisa a kasar Saudi Arebiya ya shaki iskar ‘yan ci bayan da sake shi a safiyar yau Talata.

 

Gwamnatin tarayya ce dai ta aike da tawagar mai karfi karkashin jagorancin Antoni Janar na kasa kuma Ministan Shari’a Abubakar malami da jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da lauyoyi da kuma jami’an hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna ketare tare da takwarorinsu na Jihar Zamfara don kokarin ceto Ibrahim Ibrahim.

 

Kafin sakin na sa dai sai da ya shafe tsawon shekaru uku a daure, yana fuskantar tuhumar safarar muggan kwayoyi, wanda hukuncin kisa ne a kan duk wanda aka kama a laifin a kasar Saudi Arebiya.

 

Sai dai tun da fari wasu Kotuna guda biyu a kasar sun wanke shi, amma gwamnatin kasar ta sake daukaka kara.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!