Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wasu cikin al’amuran tsaro da suka faru a shekarar 2022

Published

on

  • A ranar 5 ga Yuli ‘yan bindiga suka kai hari gidan Yarin Kuje
  • Jami’an hukumar DSS sun cafke Tukur Mamu, a ranar 6 ga Satumba
  • Gwamnatin jami’an tsaro sun cafke ‘yan ta’adda su 900

A Najeriya dai kowa ya san yadda wasu jihohin kasar ke fuskantar matsalolin tsaro da suka hada da hare–haren ‘yan Boko Haram, masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Baya ga rikicin manoma da makiyaya mai dogon tarihi, da kuma fadace-fadacen kabilanci, fashi da makami da fadan daba, har ma da tashe–tashen hankula na siyasa.

Wasu jihohin da suka fi kaurin suna a kan matsalar satar mutane domin neman kudin fansa da sun hada da Katsina, Sokoto da kuma jihar Zamfara, sai Jigawa, Bauchi, nan Kano, Filato da kuma Kaduna.

A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2022 ne al’ummar birnin tarayya Abuja suka wayi gari da jin karar harbe–harbe, wanda daga bisani aka tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga ne suka kai hari Kurkukun Kuje, tare da bude wuta a kan jama’a.

A cewar shaidun gani da ido, karar harbe–harben ta shafe kusan mintuna ashirin, wanda hakan ya sa ‘yan bindigar suka saki wasu daurarru a gidan Yarin tare da hallaka wasu mutane.

Sai dai daga bisani mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin.

Haka kuma akwai wasu jihohin kasar nan da suka fuskanci matsalar hare–haren ‘yakan Boko Haram, da suka hada da Yobe da kuma Borno.

A dai ranar 14 ga watan Mayun shekarar da ta gabata ne wasu fusatattun dalibai a jihar Sokoto suka hallaka wata daliba mai suna Deborah Yakubu, ta hanyar kunna mata wuta sakamakon zarginta da laifin yin batanci ga fiyayyen halitta.

Sai dai bayan faruwar lamarin ne Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi tur da faruwar lamarin, tare da yin kira ga al’umma da su rungumi dabi’ar zaman lafiya a Najeriya.

Haka kuma a ranar 15 ga watan Mayun ne rundunar ‘yan sandan Sokoto ta sanar da kama wadanda ake zargi da hannu wajen aikata kisan.

Wannan dalili ne ya sake tunzura wasu fusatattun matasa a jihar Sokoto har suka fara gudanar da zanga-zanga tare da kona shaguna.

A ranar 6 ga watan Satumban shekarar 2022 ne hukumar tsaro ta DSS ta kama Tukur Mamu, mai shiga tsakanin ‘yan bindigar nan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, a daidai lokacin da yake shirin zuwa kasar Saudi Arebiya daga kasar Egypt, bisa zarginsa da laifin yin alaka da ‘yan ta’adda.

Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya ya fitar, ya ce sun kama Tukur Mamu ne domin amsa wasu tambayoyi kan zargin da suke yi masa na alaka da ta’addanci.

A ranar 31 ga watan Disamban da ya gabata rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce kimanin ‘yan ta’adda dari tara ta kama da aikata laifuka daban-daban a jihar, tun daga farkon shekarar 2022 zuwa karshenta.

Rundunar ta bayyana hakan ne yayin holin ‘yan ta’addan da ta yi, wanda ta kira a matsayin na karshe da za ta gabatarwa al’ummar jihar Kaduna a shekarar da ta gabata.

Idan muka dawo nan Kano kuwa, a ranar 30 ga watan Disamban jiya ne rundunar ‘yan sanda jihar Kano ta ce daga watan Janairun shekarar da muka yi ban kwana da ita zuwa karshenta, ta samu nasarar kama mutane 136 da ake zargi da aikata laifin garkuwa mutane, da kuma wadanda ake zargi da laifin aikata fashi da makami su 125 a sassa daban-daban na Kano.

Ta cikin wata sanarwar rahoton karshen shekara da mai magana da yawunta a nan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce sun kama mutane 61 da ake zargi da laifin damfarar mutane, haka zalika sun kama manyan dillalan da ke safarar miyagun kwayoyi su kimanin 87, da kuma wadanda ake zargi da laifin satar motocin jama’a su 66.

Haka zalika ya ce rundunar ta samu nasarar cafke wadanda ake zargi da laifin satar babura mutane su 22 da barayin motoci su 10 da kuma wadanda ake zargi da laifin satar mutane zuwa wasu kasashe su 14.

Rundunar ta kara da cewa a cikin shekarar da muka yi ban kwana da ita, ta ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su, tare da ceto wasu mutane 22 da aka yi safararsu da nufin tsallakawa da su zuwa kasashen ketare.

Haka kuma sanarwar ta ce sun samu nasarar kwato bindigogi 69, ciki har da kirar AK47 guda 7 da kirar gida 7, tare da tarin alburusai da kayayyakin maye, har ma da sauran makamai kirar gida da dama.

A bangaren hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA kuwa, ita ma a ranar 30 ga watan Disamban shekarar 2022 ne hukumar ta ce ta samu nasarar dakile aikata manyan laifuka a fadin jihar Kano, musamman ma kwacen waya.

Ta cikin wani rahoton karshen shekara da jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar, dangane da irin nasarorin da hukumar ta samu a shekarar da muka yi ban kwana da ita ta 2022, ya ce sun kama masu aikata laifuka kimanin dubu uku da dari biyu da arba’in da biyar, sabanin shekarar 2021 da suka kama kama sama da mutane dubu bakwai da dari takwas, wanda hakan ya nuna cewa zuwa yanzu an samu raguwar aikata laifuka a kan hanyoyi a jihar Kano.

Haka zalika Nabulisi ya ce hukumar KAROTA ta samu nasarar yi wa Baburan Adaidaita Sahu dubu hamsin da biyu da dari biyu da arba’in da biyu rajista domin tabbatar da tsaro a Kano, kuma hakan zai bai wa fasinjoji dama wajen gano kayansu idan suka bata ko kuma idan aka aikata wani laifi da shi.

Sannan ta kama masu satar wayoyin jama’a daga cikin direbobin Adaidaita sahu da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi, baya ga nasarar kama motocin dake dakon barasa da kudinsu ya haura sama da naira miliyan dari biyar.

Haka zalika al’ummar jihar Kano ba za su taba mantawa da abinda ya faru a ranar 17 ga watan Satumban shekarar da ta gabata ba, bayan samun labarin cewa zargin wani dan kasar China mai suna Geng Quang da laifin hallaka budurwarsa mai suna Ummukulsum Buhari da aka fisani da Ummita, ta hanyar soka mata wuka.

Ita ma rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta tabbatar da faruwar lamarin.

A dai cikin shekarar 2022 da ta gabata, a ranar Talata 17 ga watan Mayu, al’ummar yankin Sabon Gari suka yi zargin cewa wani abu da suke kyautata zaton Bom ne da wani dan kunar bakin wake ya tayar, a cikin wata makaranta, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9 tare da jikkata 27.

To sai dai daga bisani rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce abin da ake zargi ba Bom ba ne, Tukunyar Gas ce ta fashe.

A dai shekarar da muka yi ban kwana da ita ne rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta karyata labarin da wata mata take yadawa a kafafen sadarwa cewa ta ga wani gungun ‘yan bindiga dauke da muggan makamai a kan Babura, har ta ce sun tsaya sun tambaye ta hanyar zuwa karamar hukumar Madobi.

SP Abdullahi Haruna shi ne mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ya ce ba za su taba mantawa da wani aikin da suka gudanar ba na bankado wata mota makare da wasu Bama–Bamai da suka kama a jihar Kano bayan da wasu bata gari suka shigo da su, da kuma batun nan da ya tayarda hankalin al’umma na kisan dalibar nan Hanifa da malaminta ya yi.

Shi ma a nasa bangaren, mai magana da yawun rundunar tsaro ta Civil Defence shiyyar Kano DSC Ibrahim Idris Abdullahi, ya ce sun samu nasarori da dama a shekarar ta 2022 musamman ma wajen dakile matsalolin rashin tsaro da kuma kama masu aikata laifuka daban–daban.

Sannan kuma ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su ci gaba da ba su hadin kai wajen ganin sun kawo karshen matsalolin tsaro a jihar Kano, a wannan sabuwar shekara da muka shiga.

Wani bangare da ke da matukar muhimmanci wajen kyautata harkokin tsaro a cikin al’umma shi ne batun bayar da hayar da gidaje haya ko sayar da filaye, la’akari da yadda ake zargin masu bayar da hayar gidaje da kuma sayarwa da laifin bai wa bata-gari wurin zama, ba tare da gudanar da cikakken bincike a kansu ba kafin ba su hayar ko kuma sayarwa.

Alhaji Adamu Usman Tambari, guda ne daga cikin masu sana’ar sayarwa da bada hayar gidaje a jihar Kano, ya ce matukar ana bukatar magance matsalar tsaro a wannan bangare wajibi ne gwamnati ta sanyawa masu irin sana’arsu doka, sannan dole ne a sanya masu rike da sarautun gargajiya cikin harkar.

Alhaji Musa Khalil Hotoro shi ne shugaban kungiyar masu bayar da hayar gidaje, sayarwa da kuma yi musu kima a Najeriya, ya ce hakika a shekarar da ta gabata an samu matsaloli masu yawan gaske a wasu jihohin kasar nan, wanda hakan ya sa dole ne ‘yan kungiyar su kara kaimi wajen kawo karshen irin wadannan matsaloli, domin kaucewa bai wa bata-gari mafaka a cikin mutane.

Ambasada Nasir Isah mai sharhi ne kan al’amuran tsaro, ya ce matukar ana fatan kawo karshen matsalolin tsaro a Najeriya wajibi ne gwamnati ta samar da ingantattun makamai ga jami’an tsaronta.

Sannan ya ce wajibi ne gwamnati ta kara tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasar nan, domin dakile kwararowar bata-gari cikin kasar, sai kuma batun fina-finan da ake shigowa da su daga ketare, da ke kara gurbata tarbiyayr kananan yara ta fuskar koyar da ta’addanci da aikata sauran miyagun laifuka.

Shekarar da mukayi bankwana da ita ta 2022 shekara ce da aka fuskanci matsalolin tsaro iri-iri a sauran sassan duniya, inda a ranar 24 ga watan Fabarairun shekarar ne kasar Rasha ta far kai wa Ukraine farmaki da nufin mamye ta, wanda har yanzu ake ci gaba da fafatawa, a wani mataki na hana kasar shiga kungiyar tsaro ta NATO.

Lamarin da ya haifar da matsalar karancin kayan abinci da kuma iskar gas ga wasu kasashen duniya.

A dai cikin shekarar da muka yi ban kwana ita ne aka hallaka tsohon Firaministan kasar Japan Shinzo Abe, ta hanyar harbinsa da bindiga a daidai lokacin da yake tsaka da jawabi a wajen taron siyasa a kasar.

 

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!