Connect with us

Labarai

Magu ya shaki iskar ‘yanci

Published

on

Dakataccen shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC, Ibrahim Magu ya shaki iskar ‘yanci

Rahotanni sun ce an sako Ibrahim Magu da yammacin ranar Laraba.

A makon jiya ne jami’an tsaron farin kaya suka tsare Ibrahim Magun, bayan da tun farko suka gayyace shi.

Tun daga lokacin ne ya fara bayyana gaban kwamitin fadar shugaban kasa domin kare kansa, game da wasu tuhume-tuhume da ake masa na zargin aikata rashawa.

A cewar rahotanni ofishin ministan shari’a Abubakar Malami na zargin Ibrahim Magu da nuna rashin da’a ga magabatansa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!