Connect with us

Labarai

Kungiyar boko haram ta kai hari sansanin sojan kasar nan a Maiduguri

Published

on

Kungiyar Bokon Haram ta kai hari sansanin sojan kasar nan dake birnin Maiduguri, yayin da suka cina wuta a wasu daga daga cikin gidajen ‘yan gudun hijira.

Kamfanin dilancin labaru na AFP ya rawaito cewa, ‘yan kungiyar sun kai harin ne a yankin Ran kilo mita 175 daga arewacin Maiduguri, kuma sun kai harin ne da yammacin jiya Litinin wanda ya tilastawa fararan hula yin gudun hijira.

Haka zalika an sami wani yunkurin da ‘yan kungiyar suka yia a yankin Magumeri kilomita 50 shima daga arewacin birnin na Maiduguri.

A halin da ake ciki a cewar hukumar dake kula da ‘yan gudun hijra ta kasa da kasa ta ce, yankin na Ran na da ‘yan gudun hijira dubu uku da dari biyar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!