Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Dangote, Adenuga, Abdussamad, arzikinsu ya karu da sama da tiriliyan 2 a shekara daya.

Published

on

Wani rahoto da mujallar Forbes da ke fitar da bayanan attajirai a duniya ta fitar, ya ce, manyan attajiran Najeriya guda uku da suka hada da: Alhaji Aliko Dangote, Mike Adenuga da kuma Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u, arzikinsu ya karu da akalla naira tiriliyan biyu da biliyan dari da saba’in da uku da miliyan goma sha uku a cikin shekara daya.

A cewar mujallar Forbes, mutanen uku sun samu jimillar dala biliyan biyar da miliyan dari bakwai tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021.

Rahoton wanda jaridar ta wallafa a jiya talata ya shafi wasu attajirai ne a nahiyar afirka guda goma sha hudu, ciki har da attajiran uku na Najeriya.

Alhaji Aliko Dangote wanda shine mutumin da ya fi kowa kudi a nahiyar afirka arzikinsa ya karu daga dala biliyan takwas da miliyan dari uku a shekarar 2020 zuwa dala biliyan goma sha daya da miliyan dari biyar a wannan shekara ta 2021, wanda hakan ya bashi damar zama mutum na dari da casa’in da daya a duniya mafi arziki.

Shi ko shugaban kamfanin Globacom da Conoil Mike Adenuga wanda shine mutum na biyu mafi arziki a Najeriya dukiyarsa ta karu daga dala biliyan biyar da miliyan dari shida a shekarar 2020 zuwa dala biliyan shida da miliyan dari daya a shekara ta 2020.

Yayin da Abdussamad Isyaka Rabi’u arzikinsa ya karu daga dala biliyan biyu da miliyan dari tara a shekarar 2020 zuwa dala biliyan hudu da miliyan dari tara a shekarar 2021.

Sauran kasashe da attajiran suka fito sun hada da Afurka ta kudu, Masar da kuma Algeria.

Dan kasar Masar Nassef Sawaris shine mutum na biyu mafi arziki a nahiyar afurka wanda ya mallaki dala biliyan takwas da miliyan dari uku.

Sai Naguib Sawiris da ya ke da dala biliyan uku da miliyan dari biyu, Muhammed Mansour dala biliyan biyu da miliyan dari biyar, Youssef Mansour dala biliyan daya da miliyan dari biyar sai kuma Yasseen Mansour da ya mallaki dala biliyan daya da miliyan dari daya.

A kasar afirka ta kudu kuwa, Nicky Oppenheimer da iyalansa sun mallaki dala biliyan takwas, Johann Rupert da iyalansa suna da dala biliyan bakwai da miliyan dari daya, Koos Bekker dala biliyan uku, Patrice Motsepe yana da dala biliyan biyu da miliyan dari tara, yayin da Michiel Le Roux ya mallaki dala biliyan daya da miliyan dari daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!