Labarai
Dangote ya shigar da karar shugaban Hukumar lura da albarkatun man fetur kan zargin al’mundahana

Shugaban matatar man fetur ta Dangote, Aliko Dangote, ya shigar da ƙorafi ga Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci a Najeria yana zargin Shugaban Hukumar lura da albarkatun man fetur, Farouk Ahmed, da cin hanci da almundahanar kudade.
A ƙorafin da ya miƙa ta hannun lauyansa, Dangote ya buƙaci a kama, bincika tare da gurfanar da Farouk bisa zargin kashe fiye da dala miliyan bakwai wajen karatun ‘ya’yansa a Switzerland, ba tare da sahihin tushen kuɗi ba.
Jaridar Punch ta ruwaito Dangote ya ce Farouk ya yi amfani da mukaminsa wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati don amfanin kansa, lamarin da ke saɓa wa dokar rikon amana ga jami’an gwamnati.
Inda ya bukaci ICPC ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin kare gaskiya da martabar gwamnati a kasar.
You must be logged in to post a comment Login