Labarai
Gwamnatin Kano ta ware miliyan 345 domin ciyarwar azumin Ramadana mai kamawa
Kwamishinan yada labarai Kwamred Muhammad Garba wanda shi ne shugaban kwamitin ciyarwar shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi yayin taron kaddamar da shirin ciyarwar azumin watan Ramadana na bana, wanda ya gudana a nan Kano.
Kwamred Muhammad Garba ya ce gwamnatin jihar Kano ta ware kudaden ciyarwar ne domin tallafa wa marasa karfi a watan na Ramadana.
Ya kuma ce, kwamitin zai rika sanya ido kan shirin, game da yadda ake raba abinci ga mabukata.
Kwamishinan yada labaran ya kara da cewa duk wanda aka kama da yin ha’inci daga cikin wadanda aka dauka kwangilar girkin abincin, ko kuma masu rabon abincin, shakka babu za’a karbe aikin daga hannun su.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar yada labarai Sani Abba Yola ya fitar, ta ruwaito kwamishinan na kira ga masu hannu da shuni da su rika taimakawa mabukata, musamman ma a wannan lokaci.