Connect with us

Labarai

Gwamnatin tarayya ta sanya hannu a kwantiragin fiye da dala miliyan 6 da wani kamfanin China

Published

on

Gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan wani kwantiragin Dala biliyan 6 da miliyan 68 da wani kamfanin kasar China don gina layin dogo daga garin Badin zuwa Kaduna, daga cikin aikin layin dogon da ya tashi daga Lagos zuwa Kano.

Wannan jawabi na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktar yada labaran ma’aikatar Sufuri Yetunde Sonaike ta bayan jiya a Abuja, tana mai cewa Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar don fara aikin na Badin zuwa Kaduna.

A cewar sanarwar ministan ya shaida cewa aikin zai kammala ne cikin wa’adin shekaru biyu zuwa uku, kuma ma’aikatar za ta samar da kudaden da ake bukata a cikin kasafin kudin bana da na badi.

Layin dogon zai bi ta garin Oshogbo zuwa Ilori zuwa Minna, yayin da wani layi guda daga Oshogbo zai bi ta Ado-Ekiti.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,747 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!