Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Dino Melaye: karramawar da shugaba Buhari yayi wa MK Abiola abu ne mai kyau

Published

on

Sanata Dino Melaye da ke wakiltar Kogi ta tsakiya ya ce karramawar da gwamnatin tarayya ta yiwa MKO Abiola abu ne da ya da ce da kuma aka yi shi a lokacin da ya da ce.

 

Sai dai a baya Dino ya kalubalanci matakin bada lambar yabo ta GCFR ga Abiola, inda ya ce bai kamata a baiwa mamacin wannan lambar yabo ba.

 

A cewar sa duk yadda al’amura suka kai da kyau, dokar kasa dole ta tsaya a dokar kasa,  inda ya ce sashi na biyu na kundin tsarin mulkin kasar nan ya bada damar karrama duk wanda aka ga dama matukar dan kasa ne, sai dai mamaci ba dan kasa ba ne.

 

Sai dai Dino a jawabin da ya fitar a jiya Lahadi yayi amai ya lashe inda ya ce akwai bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana MKO Abiola a matsayin wanda ya lashe zaben na June 12.

 

Ya kuma bukaci hukumar zabe ta kasa INEC da ta ayyana zaben na ranar 12 ga watan Yuni a hukumance.

 

Inda kuma ya bukaci hukumar zartarwa ta kasa da ta nemi damar yin gyara a cikin kudin tsarin mulkin kasa da zai bada damar karrama Abiolan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!