Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Nigeria da kasar Morocco sun amince kan yarjejeniyar safarar iskar gas

Published

on

Nigeria da kasar Morocco sun amince da sanya hannu domin tabbatar da yarjejeniyar kafa bututun safarar iskar gas zuwa yankin Arewacin Africa zuwa gabar kogin Atlantic da suka yi a baya.

 

Kafar sadarwa ta kasar morocco ta ruwaito cewar manyan jami’an gwamnatin kasashen biyu ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya a  birnin Rabat na kasar Morocco lokacin da suke karin bayani kan yadda za a inganta yarjejeniyar da aka cimma tun a shekarar 2016.

 

Kasashen biyu sun amince da lalubo hanyar da za yi kari kan bututun iskar gas da ya tashi daga kudancin kasar nan da ya ketare ta kasar Benin, yabi ta Togo ya kuma tuke a kasar Ghana tun a shekarar 2010.

 

Wannan batu dai na samar da bututun iskar gas daga Najeriya zuwa yankin Arewacin Africa batu ne da aka dade ana bukatar sa tun wani lokaci mai tsaho.

 

Ko a baya kasar Algeria ta tattauna batun da kasar nan tun a shekarar 2002 kan samar da bututun iskar gas din, sai dai kasar ta Algeria ta gaza daukar nauyin gudanar da aikin.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!