Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar kula da gidajen yari ta kasa ta ce ba gaskiya bane cewar fursunoni sun fasa gidan yari a Minna

Published

on

Hukumar kula da gidajen yari ta kasa, ta ce; ba gaskiya bane cewa fursunoni sun fasa gidan yarin garin Minna a makwan jiya.

 

A cewar hukumar, lamarin da ya faru a kwanakin baya hari ne kawai aka kai gidan yarin amma ba fursunoni ne suka fasa gidan yarin ba.

 

Mai magana da yawun hukumar Francis Enobore shi ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.

 

Ya ce ya zama wajibi hukumar ta wayar da kan al’ummar kasar nan musamman wadanda ke cewa fursunoni ne suka fasa gidan yarin suka tsere.

 

A baya-bayan nan ne dai wasu ‘yan bindiga suka kai hari ga gidan yarin da ke garin Minna, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani jami’in hukumar daya da kuma wani mutum da ke tafiya akan babur kusa da gidan yarin.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,961 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!