Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Direbobi za su cigaba da baiwa gwamnati hadin kai – NURTW

Published

on

Kwamitin riko na kungiyar masu motocin sufuri na haya da daukan kaya ta kasa RETEAN/NURTW ya hori direbobi kan su ba wa gwamnati hadin Kai wajen ci gaba da bin dokokin hanya tare da magance zaman kashe wando tsakanin matasa.

Sabon shugaban kwamitin reshen Jihar kano Alhaji Ja’e Na Almu ne ya ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da mambobin kungiyar domin tabbatar musu da kudirin su na kara kyautata wa fasinjojin da samar musu da saukin kudin sufurin yau da kullum a duka tashoshin su.

Haka kuma ya nemi goyon bayan mambobin kan tallafa musu domin ganin kwamitin rikon ya samu nasarar da yakamata.

Shi ma anasa bangaren daya daga cikin mahalarta taron Alhaji Danladi Baba Kwanar Dawaki bayyana gamsuwar su ya yi kan irin kudirin kwamitin rikon, tare da neman agaji gwamnati ga Mambobin nasu ta yadda za su samu sarara wa daga matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Wakilin mu Sani Ahmad Sagagi ya rawaito mana cewa dubban mambobin kungiyar ne suka halarci taron daga dukkanin rassan kungiyar dake Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!