Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Doka ta haramta ajiyewa ko kashe dabbar daji -MD ZOO

Published

on

Manajan daraktan Hukumar Kula da gidajen ajiye namun daji da aka fi sa ni da gidan “Zoo” Alhaji Sadik Kura Muhammad ya gargaɗi al’umma da su guji ajiye dabbobin daji a gida.

Haka kuma ya yi kakkausan gargaɗi ga masu yin wasa da dabbobin daji a matsayin sana’a.

Sadik Kura Muhammad ya yi wannan gargaɗi a wani taron manema labarai da ya kira a ranar Laraba, biyo bayan rahoton da aka samu na ɓallewar wata Kura a garin Ɗanbatta, har ma wasu mafarauta suka kashe ta.

Tun da fari dai Al’ummar garin Fagwalawa a ƙaramar hukumar Ɗanbatta a jihar Kano, sun shiga cikin zulumi sakamakon bayyanar wata Kura a cikin garin.

Hakan ne ya sanya wasu mafarauta a yankin suka yi nasarar kashe kurar tare da yin bandarta.

Wannan dai shi ne karon farko da aka taba samun bayyanar Kura a cikin ƙauyen na Fagwalawa wanda kuma har kawo zuwa wannan lokacin ba’a san daga inda ta fito ba.

Bayan samun labarin ne Manajan Daraktan kula da gidajen adana namun daji Alhaji Sadik Kura ya ce “Doka ta haramta ajiye kowanne irin nau’in dabbobin daji a gida, kuma yin haka ya saɓa doka don haka duk wanda aka samu da wannan laifin za a gurfanar da shi a gaban kotu”.

“A yanzu yin wasa da namun daji a matsayin sana’a da wasu mutane ke yi a unguwanni da kasuwanni, mun soke shi kuma idan aka kama mutum da laifin hakan za a iya yankewa mutum hukuncin zaman gidan yari har ma da tara” a cewar Kura Muhammad.

Ya kuma ce, Idan har ma mutum yana da sha’awar ajiye dabbar daji a gida sai ya nemi izinin hukumar kula da namun daji kuma sai an tabbatar da wajen da zai ajiye don ganin cancantarsa da kuma kare rayukan Al’umma.

Ko da aka tambaye shi ko shin daga ina yake zargin Kurar ta fito? Sadik Kura Muhammad ya martani da cewa “yankin Ɗanbatta ba wajen da Kura ta ke an yin rayuwa ba ne domin yana da rairayi sosai, kuma wajen ya yi nisa da dajin Falgore bare a ce daga nan ta gudo,don haka muna da yaƙinin ta kufce daga hannun masu kiwonta a gida ba bisa ƙa’ida ba”.

Sai dai ya jaddada cewa doka za ta hukunta duk wanda aka kama da laifin kashe dabbobin daji, domin hakan yana taƙaita yawaitar su, don haka duk wanda ya ga dabbar dawa ya yi ƙokarin sanar da hukumomi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!