Labarai
Dokar bai wa mata damar samun gurbi a majalisun kasar nan za ta tsallake karatu na biyu
Kudirin dokar da zata tilastawa kowacce jiha ta ware kujera daya ga mata a matsayin ‘yar majalisar dattijai, za ta samu karatu na biyu nan ba da jimawa ba a zauren majalisar wakilai.
Yar majalisa Taiwo Oluga, wadda ita ce shugabar Kwamitin kula da al’amuran mata a majalisar, ta bayyana hakan lokacin da ta ke karbar bakuncin Kungiyar da ke rajin samar da daidaiton jinsi a Abuja.
Yar majalisar ta ce kudirin wani shiri ne na kwamitin kuma na daga cikin bangare na kokarin karawa mata wakilci a cikin gwamnati.
Taiwo Oluga ta kara da cewa kunshin dokar ta bukaci a samu akalla sanata daga kowace jiha, mafi karanci ya zama biyu cikin uku.
A cewar ta matukar aka sanya mata a cikin al’amuran majalisa to kuwa za su bada gudunmawa wajen ci gaban al’amuran kasa kamar tsaro, kiwon lafiya da kuma rage yawan yara da ba sa zuwa makaranta.
You must be logged in to post a comment Login