Labaran Kano
Dokar hana goyo kan babur na nan daram – KAROTA
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta bayyana cewar dokar hana goyo a kan babur da aka sanya a jihar na nan daram.
Shugaban hukumar Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio na yau, wanda ya mayar da hankali kan harkokin sufuri a nan Kano.
Baffa Babba Dan gundi ya kuma ce an sanya dokar skamakon yadda wasu masu baburan ke gudanar da sana’ar Acaba a lokacin da ake zaman gida sakamakon dokar hana zirga-zirga da aka sanya.
Ya kuma kara da cewar jami’an ‘yan sanda na taimakawa jami’an hukumar wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata ba tare da wata tangarda ba.
Shugaban hukumar ta KAROTA ya bayyana cewar hukumar za ta ci gaba da kamawa tare da gurfanar da duk wanda ta kama da laifin karya doka a gaban kotu, domin hukunta shi dai-dai da laifinsa.
You must be logged in to post a comment Login