Connect with us

Labaran Kano

Ma’aikatan KEDCO sun rasu sanadiyyar hatsari

Published

on

Wasu ma’aikatan kamfanin rarraba wutar lantarki shiyyar Kano KEDCO guda biyu sun rasa rayukan su, sanadiyyar hatsarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar su ta dawowa Kano daga jihar Katsina.

Hakan na cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na kamfanin Ibrahim Sani Shawai ya fitar.

Sanarwar ta ce, wadanda suka rasun sun hada da Malam Nazir Ahmad da Malam Abdurra’uf Ahmad.

Sanarwar ta kara da cewa, hatsarin ya faru ne sakamakon fashewar tayar motar a karamar hukumar Kankiya wanda yayi sanadiyyar hatsarin, tare da jikkata mutane shida.

Yayin da direban motar da wani guda mai suna Mr Johnson suka tsira ba tare da samun  ranuni ba.

Kazalika, sanarwar ta bayyana cewa tuni aka dauko gawarwakin wadanda suka rasu zuwanan  Kano don yi musu jana’iza sauran kuma aka kai su asibiti don ci gaba da duba lafiyar su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!