Labarai
Dokar hana yara amfani da social media a Australia ta fara aiki

A yau ne dokar hana yara amfani da shafukan sada zumunta ta fara aiki a Austiraliya.
Firaministan ƙasar Anthony Albanese, ya bayyana dokar a matsayin abin alfahari ga kasar yana mai cewa za ta shiga tarihi muhimmancin kawo sauyi, da ya ce ƙasar sa na kan gaba a duniya wajen ɗaukar wannan mataki.
Yara ’yan ƙasa da shekaru 16 sun tarar an rufe musu shafukan su a manyan dandali 10 ciki har da TikTok da Snapchat.
Sai dai ko a rana ta farko, rahotanni sun nuna cewa da dama daga cikin su suna samun hanyoyin kaucewa wannan dokar.
Kamfanin Meta, mammallakin Instagram da Facebook, ya ce dokar na tura yara zuwa wasu shafuka da ba su da tsauraran dokoki.
You must be logged in to post a comment Login